Labarai
COVID-19 : Ana daf da bude makarantun Islamiyya a Kano
Hukumar Kula da Makarantun Islamiyya ta jihar Kano ta bukaci Malaman Islamiyya da dalibai da su kara hakuri don kuwa gwamnati na dab da kammala tattaunawa da jami’an lafiya domin bude Makarantu baki daya.
Shugaban hukumar Sheikh Gwani Yahuza Gwani Danzarga ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema labarai a nan Kano.
Sheikh Gwani Yahuza ya kara da cewa gwamnatin Jihar Kano, ta damu matuka ganin yadda daliban ke zaune a cikin gidajensu, ba tare da karatun Addini da na Islamiyya ba.
Shehin Malamin ya kuma ce,annoba gaskiya ce saboda hakane ma All.. yayi umarnin cewa duk lokacin da annoba ta bullo to wajibi ne a dauki matakan kariya domin kare al’umma.
Labarai masualaka :
Babu wanda ya rasa ran sa a cikin masu dauke da cutar Corona a Kano
Ganduje ya fara daukar Malaman da zasu yi koyarwa a makarantun Tsangayu
Wakilinmu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa, shugaban hukumar na kira ga al’umma da su ci gaba da bin dokokin da jami’an lafiya suka shinfida musu.
You must be logged in to post a comment Login