Coronavirus
Covid-19: Anyi sulhu da ‘yan Kasuwa kan tashin kayan masarufi a Kano
Rahotonni a nan Kano na cewa an cimma matsaya tsakanin ‘yan Kasuwar kayan masarufi ta Singer da kuma hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta Kano.
A farkon makon da muke ciki ne, hukumar yaki da rashawan ta Kano ta sha alwashin kwace kayayyakin ‘yan kasuwar da aka samu sunyi karin kudi akan kayayyakinsu.
Sai dai sakamakon wani sumame da jami’an hukumar yaki da rashawar sukayi a dakunan ajiyar ‘yan Kasuwar, sun samu nasarar kame wasu kayayyaki da ake zargin an boyesu.
A ranar Talata ne dai gamayyar ‘yan Kasuwar suka ziyarci hukumar ta yaki da rashawa inda akayi zaman sulhu domin samun dai-daito.
Wani dan Kasuwar ta Singer, Alhaji Ibrahim Danyaro ya shaidawa Freedom Radio cewa matsalar karin kudin kayayyakin ba daga wurinsu bane domin kuwa mafi yawa manyan kamfanunuwan da suke siyan kayayyakin sune suke yi musu kari.
Har ila yau, Alhaji Danyaro ya ce kamfanin BUA ne kadai basa yi musu karin kudi.
Karin labarai:
An samu cunkoso a kasuwannin Kano
Babu hannu na a musgunawa ‘yan kasuwannin Kwari da Sabon Gari – Ganduje
A nasa bangaren shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce yanzu haka sun cimma matsaya da ‘yan Kasuwar babu wani batu na kara samun tashin farashin kayayyaki a nan gaba.
Idan zaku iya tunawa dai a makon da ya gabata ne aka samu tashin farashin kayan masarufi lokacin da gwamnatin Kano ta sassauta dokar kulle a jihar.
Haka kuma acikin makon da ya gabatan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gayyaci ‘yan Kasuwar inda ya ja musu kunne akan su gujewa karin farashi ga jama’a.
You must be logged in to post a comment Login