Labaran Wasanni
COVID-19: Bikin kakar wasanni ka iya zama barazana ga lafiyar al’umma
Masana kiwon lafiya sun gargadi hukumar kwallon kafa ta Najeriya kan batun gudanar da gasar bikin kakar wasanni ta shekarar 2020 yayin da ya rage saura makwanni uku a fara.
Za dai a gudanar da bikin kakar wasannin ne a ranar goma sha hudu zuwa ranar ashirin da takwas ga watan Faburairu a garin Benin dake jihar Edo.
Masana kiwon lafiya na ganin cewa gudanar da gasar ka’iya zama barazana ga lafiyar al’umma duba da yadda annobar Coronavirus data dawo kuma take ci gaba da yin kamari a fadin kasar nan.
Rahoto na cewa, kawo zuwa ranar 26 ga watan Janairu yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya ya kai 122,996 yayin da kuma cutar ta kashe mutane 1,509.
Ana dai tsammanin ‘yan wasa da jami’ai kimanin 15,000 za su hallaci wajen gudanar da bikin kakar wasanni a jihar ta Edo.
You must be logged in to post a comment Login