Labarai
Covid-19: Buhari zai dawo da ‘yan Najeriya mazauna kasar China
Ofishin jakadancin kasar nan da ke birnin Beijing a kasar China, ya Ce, gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shirye domin fara jigilar yan kasar nan mazauna can domin dawo da su gida Najeriya.
A cewar ofishin daukar wannan mataki ya biyo bayan fitar wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ya nuna yadda hukumomi a
birnin Guangzhou suka fatattaki wasu ‘yan kasuwar kasar nan da dalibai da ke karatu a can kasar ta China daga dakunan Otal dinsu.
Rahotanni sun ce birnin Guangzhou shine gari da al’ummar Afirka suka fi ziyarta domin gudanar da harkokinsu na kasuwanci a kasar ta China.
LABARAI MASU ALAKA
Yadda cutar Corona Virus ta shafi ‘yan Najeriya a kasar China
Covid-19: Buhari zai rabawa al’ummar Kano sama da naira biliyan daya
Covid-19: Coronavirus na iya kawo karayar tattalin arziki a Najeriya -Buhari
A cikin faifan bidiyon dai al’ummar Najeriyar sun yi ikirarin cewa bayan fatattakar su daga masaukan nasu da hukumomin birnin su ka yi, basu samar musu da wani waje na daban ba, sannan ba a basu abinci ba.
Wani dalibi dan asalin kasar nan wanda yana daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, ya shaidawa gidan talabijin na BBC cewa, akwai ‘yan kasar nan sama da dari watse akan tituna babu abinci babu masauki.
Ko a shekaran jiya Alhamis ministan harkokin kasashen waje na kasar nan Geoffrey Onyeama ya shaidawa manema labarai cewa ya gayyaci jakadan kasar ta China a Najeriya, Mr. Zhou Pingjian domin jin dalilan da ya sa hukumomi a birnin na Guangzhou su ka ji zarafin al’ummar kasar nan mazauna can.
You must be logged in to post a comment Login