Kiwon Lafiya
Covid-19: Coronavirus na iya kawo karayar tattalin arziki a Najeriya -Buhari
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce bullar cutar Corona ta kara kawo tabarbarewar tattalin arziki a kasa musamman a bangaren samar da danyan man fetur.
Buhari ya bayyana hakan ne yayin da kungiyoyin ma’aikatan lafiya suka kai masa masa ziyara a fadarsa ta Villa dake garin Abuja game da matsalolin da suke fama dashi.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Muhammad Buhari, ya bukaci ma’aikatan lafiyar da su kara hakuri da gwamnatin sa game da bukatun al’umma a kokarin ganin an magance cutar Corona.
Ya kuma ce matsalolin su ya zama wajibi a dubesu duba da muhimmancin da suke dashi ga rayuwar al’umma, adon haka ya kamata su saka a ransu cewa a yanzu komai baya tafiya yadda ya kamata sakamaon bullar cutar Corona.
Ya ce matsalar Corona ta shafi harkokin manfetur da kasar nan ta dogara a kansa wajen samar mata da kudaden shiga.
Kungiyoyin ma’aikatan lafiyar dai na bukatar gwamnatin tarayya data gyara dokar da ake biyan ma’aikatan lafiya albashi a kasar nan musamman ta yadda za’a kara inganta musu albashin su.
You must be logged in to post a comment Login