Manyan Labarai
Covid 19- Fitilar Bichi ta raba kayan tallafi
Kungiyar cigaban al’ummar Bichi, Fitilar Jama’ar Bichi, ta raba Robobin wanke hannu, Sabulai, da Sindarin tsaftace hannu ,hade da takunkumi da sauran kayan daukar matakan kariya daga cutar Corona tare da bayanai na kare kai daga kamuwa da cutar.
Daga cikin guraren da aka raba kayan sun hada da Asibitin Bichi, gidan gyaran hali wato Kurkuku, Gidan Sarki, da Masallacin Saye da na Badume.
Da yake jawabi a yayin bada kayan tallafin , shugaban Fitilar Jama’ar Bichi Alhaji Rilwanu Idris Malikawa Garu, ya ce tallafin anyi shi ne domin amsa kiran gwamnati na yakar cutar da kuma dakile yadauwar ta.
Labarai masu alaka.
Covid-19: Buhari zai rabawa al’ummar Kano sama da naira biliyan daya
Covid-19: Ban san me ya hada 5G da Coronavirus ba – Pantami
Rilwanu Idris Malikawa Garu, ya da da da cewa kungiyar zata kuma yi makamancin wannan rabon, a cikin karshen mako a yankin Danzabuwa, tare da yin addu’ar Allah ya kawo karshen wannan Annoba, da baiwa wanda suka kamu da cutar lafiya.
A nasa jawabin mataimakin Darakta na Asibitin Bichi, Alhaji Muhammad Abdullahi, ya yabawa kungiyar bisa kokarin da suke a yankin na Bichi, don ganin cigaban yankin da tallafwa marasa galihu.
Muhammad Abdullahi, ya yi kira ga al’umma dasu guji zuwa Asibitoci domin duba marasa lafiyar da ka kwantar, don gudun yada cututtuka.
You must be logged in to post a comment Login