Labarai
COVID : 19 – Ganduje ya gana da sarakuna da malamai
Biyo bayan sake bullar cutar COVID-19 a sassan duniya a karo na biyu, jihar Kano ta bayyana cewar mutane goma sha bakwai ne suka rasa rayukan su ta sanadiyar cutar tun daga watan Disambar bara zuwa Janairu, 2021.
Mataimakin babban jami’i kwamitin Kar ta kwana Kan yaki da Corona Dakta Sabitu Shuaibu Shanono ne ya bayyana hakan a ya yin da Gwamnan Kano ke ganawa da sarakuna guda biyar da hakimai dangane da sake dawowar cutar Karo na biyu.
Dakta Shanono ya ce daga watan Nuwamba 2020 zuwa Janairu, 2021, jihar Kano ta samu sabbin wadanda suka kamu da cutar har 827 tun bayan da Annobar ta biyu ta zo don haka ya yi kira ga Sarkunan don wayar da kan jama’a kan yadda za su Kare kansu.
A nasa bangaren Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce, gwamnatin ta kirawo sarakunan gargajiya da kuma malamai a jihar saboda su suka fi kusa al’umma adon haka ya ce su wayar da Kan mutane yadda zasu Kare kansu
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta hada kai da jami’an tsaro don tabbatar da cewar ana bin kaidojin cutar.
TWakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan na Kano Kuma shugaban kwamitin COVID-19, Nasiru Yusuf Gawuna.
Ya ce gwamnatin jihar za ta raba abin rufe fuska miliyan 2 a dukkanin masarautu 5 da ke jihar.
You must be logged in to post a comment Login