Labaran Kano
Covid-19: Ganduje zai fara raba tallafin kayan abinci
Kwamitin da gwamnatin jihar kano ta kafa na neman taimakon kan bullar cutar corona ya bayyana cewar tsare-tsare sun yi nisa domin ganin an fara gudanar da raban kayayyakin abincin da aka tara domin tallafawa al’ummar jihar Kano, a wani bangarena rage musu radadin halin da suke ciki game da annobar cutar Covid-19.
Farfesa Mahammad Yahuza Bello wanda shine shugaban kwamitin, kuma shugaban Jami’ar Bayaro dake nan kano, na ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan freedom radiyo wanda ya mayar da hankali kan tattaunawa da kuma Karin bayani kan kayayyakin da kwamitin ya samu zarafin Tarawa zuwa yanzu
Farfesa Mahammad Yahuza Bello ya kara da cewar an samu taimakon nau’in kayan abinci kimanin buhu dubu uku da dari uku kuma kayan amfani a bangaran kiwon lafiya da suka hadar da sabulun wake hannu sanitizer da darajar kudin say a kai naira miliyan dari uku da sabain da shida.
Shugaban kwamitin ya kuma kara da cewar za’a raba kayyayakin ga mutane dubu 50 a fadin jihar nan yadda ya kamata batare da samun wani tsaiko ba.
Mahammad Yahuza Bello ya kuma yi kira da dukkanin wanda yake da iko da ya tallafawa jama’a a dai-dai lokacin da mutane ke neman taimako, bayan da aka tilasta musu zaman gida don takaita yaduwar Corona.
You must be logged in to post a comment Login