Kiwon Lafiya
Covid-19 Gwamnatin Kano ta ja hankalin jama’a kan tsaftar muhalli
Hukumar lura da asibitoci da dakunan binciken lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano ta bayyana cewa babu mamaki idan har aka dade ba a gano maganin warkar da cutar corona ba duk kuwa da kokarin yin haka da masana a fadin duniya suka dukufa wajen ganp maganin nata.
Shugaban hukumar, Dakta Usman Aliyu ne ya bayyana haka a cikin shirin ‘Barka da Hantsi’ na tashar Freedom Radio.
Dakta Usman Aliyu wanda ya ce har yanzu masu bincike na duniya sun gaza gano maganin wannan cutar, ya ja hankalin jama’a da su kara lura sosai da kuma samarwa kansu kariya domin kaucewa kamuwa da cutar.
Usman Aliyu wanda kuma kwararren likita ne ya bukaci dukkan ma’aikatan asibtoci a jihar Kano da su tabbatar da marasa lafiya na samun irin kulawar da ta kamace su musamma ma a wannan lokacin da ake fama annobar Covid-19.
Shugaban hukumar ya ja hankalin jama’a kan tsaftar jiki da ta muhallansu da kuma yin amfani da shawarwarin jami’an lafiya don kare kawunansu daga cutuka masu saurin yaduwa, ba wai Covid-19 kadai ba.
You must be logged in to post a comment Login