Kiwon Lafiya
Covid 19: Gwamnatoci su kara kokari-Dakta Muhammad Abdu
Wani likitan Dabbobi Dakta Muhd Abdu, yace cutar Corona ta hana masu kiwo sakewa wajen nemo abincin dabbobi harma da masu sana’ar noma da da sauransu.
Muhammad Abdu ya bayyana haka ne ta cikin shirin Duniyar mu a yau na nan Freedom Rediyo
Likitan yace gwamnati na da rawar da zata taka wajen taimakawa al’ummar kasar nan musamman tallafin kayan abinci da kayan noma da makamantan su.
Labarai masu alaka.
Wasu ‘yan Najeriya sun kamu da cutar COVID-19 a kasar Sin
Killace kai da hana Sallah a cikin jama’a lokacin Annoba dai -dai ne a Musulunci
A nasa jawabin Alhaji Abdulkadir Mustapha, wanda ya kasance cikin shirin kuma babban manomi a nan jihar Kano yace noma a kasar nan yaja baya ba kamar lokacin baya ba da kayan abinci suka wadata, sai dai yanzu kayan basa siyuwa a kasuwanni sabo da bullar cutar ta covid 19
Bakin sunyi kira da Gwamnato ci a dukkan matakai dasu maida hankali wajen yakar cutar don samun kwanciyar hanakali tare da dawowa harkoki kamar yau da kullum.
You must be logged in to post a comment Login