Connect with us

Coronavirus

Masu Corona sun haura 400 a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa mutane 427 ne suka kamu da cutar Covid-19 a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ta sanar a shafinta na Twitter cewa a ranar Laraba an samu karin mutane 30 da suka kamu da cutar a jihar.

Har ila yau, ma’aikatar lafiyar ta Kano ta ce an samu karin mutane 3 da aka sallama bayan sun warke daga cutar, yanzu haka mutane 6 ne suka warke daga Coronavirus a jihar Kano.

Sanarwar ma’aikatar lafiyan tace an samu karin mutane 5 da suka rasa ransu sanadiyyar cutar ta Corona, wanda ya kai adadin wadanda cutar ta hallaka a jihar zuwa mutane 13.

Karin labarai:

Yadda mutane 3 na farko suka warke daga Corona a Kano

Yadda Likitoci 34 suka kamu da Corona a Kano

Yanzu haka dai mutane 408 ne ke dauke da cutar wadanda suke karbar kulawa daga wurin jami’an lafiya.

Jihar Kano dai ita ce jiha ta biyu a jihohin dake da yawan wadanda suma kamu da cutar ta Covid-19 a kasarnan.

Ko a ranar Talatarnan an tabbatar da cewa likitoci 34 ne suka kamu da cutar ta Covid-19 a jihar ta Kano.

Yayinda a ranar Laraba kuma rahotonni suka tabbatar da cewa ma’aikatan jinya da Ungozoma 18 ne suka kamu da cutar ta Covid-19 a Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,403 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!