Labarai
Covid-19: Za a rufe makarantu a jihohin Arewa masu yamma
Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma sun ce za su rufe daukacin makarantun dake yankin daga ranar Litinin mai zuwa, saboda annobar cutar Coronavirus.
Shugaban kungiyar Gwamnonin yankin Arewa maso yamma, Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ne ya bayyana hakan, ta bakin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi wanda ya yi jawabi a madadinsa, yayin wani taro da gwamnonin suka gudanar a jihar Kaduna.
Wakilin mu a Kaduna Babangida Aliyu Abdullahi ya rawaito mana cewa gwamnonin sun yi taron ne a fadar gwamantin jihar Kaduna a yau Laraba.
Karin labarai:
COVID-19 : Tambuwal ya dakatar da bajakolin nuna al’adu
Kano: Babu rahoton bullar cutar COVID-19 -Dr, Aminu Tsanyawa
Taron ya samu halartar Gwamnonin jihohin Katsina, da Kebbi, da Kaduna, da jihar Jigawa, da Zamfara, sai kuma jihohin Sokoto, da Niger.
Mataimakin Gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna shine ya wakilce gwamnan Kano a taron.
Sai Gwamnan jihar Kwara dake yankin arewa ta tsakiya wanda ya bugo waya yace sun aminta da duk matakin da Gwamnonin yankin arewa maso yamma suka dauka, kasancewar shugaban Gwamnonin arewa ta tsakiya wato Gwamnan jihar Niger Muhammafd Sani Bello ya halarci wannan taro.
You must be logged in to post a comment Login