Labarai
Covid19: Babu dan kasar nan daya kamu da cutar Corona Virus.
Gwamnatin tarayya tace babu wanda ya kamu da cutar Corona Virus, a cikin mutum goma sha hudu da suka yi mu’amala da wanda ya shigo da cutar cikin kasar nan .
Ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire , ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja yau, a yunkurin da ake na hana bazuwar cutar cikin kasar nan.
Cutar mai lakabin Covid 19, dan kasar Italiya ne ya shigo da ita kasar nan ranar ashirin da biyar ga watan Fabrairun da ya gabata, bayan dan takaitaccen zuwan harkokin kasuwanci da ya yi.
An kai rahoton mutumin tare da killace shi a Asibitin cututuka masu yaduwa dake Yaba ta jihar Lagos.
Dakta Ehanire , ya ce zuwa yanzu haka gwamnatin tarayya na aiki kafada da kafada da jihohin Lagos da Ogun ,don bincikawa da gano hanyoyin dakile cutar.
Wanda a halin yanzu an gano cewa dan kasar Italiyan ya yi mu’amala da mutum sha Tara a Lagos da kuma ashirin da Tara a jihar Ogun ,ciki har da direban da ya dauko shi daga filin jirgin sama.
Covid19: Gwamnatin Kano ta samar da lambobin kira kan Coronavirus
Dalilan dakatar da wasanni a birnin Tokyo
Kasar Saudiya ta dakatar da zuwa Umara
Ya ce zuwa yanzu haka gwamnatin jihar Plateau ta bayyana tsare wasu yan kasar China su hudu, da ake zargin suna da cutar ,sai dai binciken da aka gudanar ya nuna basu kamu da cutar ba.
Kuma an killace su na kwana talatin don ganin yadda zasu kasance a tsawon wannan lokaci, tare da kuma bibiyar yadda yanayin yadda cutar take a kasashen duniya.
Ministan ya yi kira ga ‘yan kasar nan dasu zauna a gida matukar sunji canjin yanayi na rashin lafiya a jikin su, musamman ma tari, zazzabi da matsalar numfashi.
Sannn yace a kira lambar kar ta kwana ta Cibiyar lura da takaita cututuka ta kasa (NCDC), akan wannan lamba 0800 970 0000-0010.
Kamfanin dillancin labarai na kasa nan, ya ruwaito cewa zuwa yanzu haka ,kasar nan ita ce kasa ta uku data samu bullar cutar mai lakabin Covid 19, a nahiyar Afirka ,bayan kasar Misrah wato Egypt da Algeria .
You must be logged in to post a comment Login