Manyan Labarai
Cutar Kwalara ta sake bulla kasar Kamaru
A ranar Laraba gwamnatin kasar Kamaru ta bayar da sanarwar bullar cutar Kwalara a kasar tare da yin sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Rahotonni sun bayyana cewa wadanda suka kamu da cutar ya zuwa yanzu sun kai mutum 62 cikin mutane 83 da tun da fari aka yi zargin sun kamu da cutar a wani kauye, yayin da sha-biyu daga ciki suka rasa rayukan.
Gwamnan lardin da lamarin ya faru, Felix Nguele wanda ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai ya ce a yanzu haka an fara gudanar da allurar rigakafi a yankin da kwalarar ta bulla.
Nguele, ya kara da cewa wannan ne karon farko da ta bulla a watannin da suka gabata, inda ta hallaka mutane da dama ba tare da gano dalili ba, sai yanzu.
Sai dai hukumomin lafiya a kasar na zargin gurbatar muhalli a yankunan ne ya haifar da matsalar musamman a yankin Londji.
You must be logged in to post a comment Login