Addini
Da ɗumi-ɗumi: Majalisar dokokin Kano ta buƙaci DSS su sanya ido kan Baffa Hotoro
Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya umarci hukumar tsaro ta DSS da rundunar ƴan sandan Kano su sanya ido a kan Malamin nan Baffa Hotoro tare da gurfanar da shi a gaban hukumar Hisbah da majalisar Malamai sakamakon kalaman ɓatanci da ya yi a kan mutanen garin Tudun Biri da harin jirgin sojin sama ya hallaka.
Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan ƙudurin gaggawa da wakilin ƙaramar hukumar Ƙiru a zauren Usman Abubakar Tasi’u, ya gabatar yayin zaman majalisar na ranar Litinin.
Ɗan majalisar na Ƙiru, ya ce, kalaman da Baffa Hotoro ya furta ga mutanen da iftila’in ya ritsa da su sun yi muni matuka, don haka ya kamata a ɗauki mataki a kansa.
Bayan ganawa ta musamman da mambobin majalisar suka gabatar kan wannan batu ne suka amince baki ɗaya da zauren ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta ɗauki waɗannan matakai guda huɗu a kan Malamin don gudun tada fitina.
You must be logged in to post a comment Login