Labaran Kano
Da dumi-dumi ana rikici a majalisar dokoki ta Kano
Rikici ya barke ne ya biyo bayan wani kudiri da daya cikin ‘yan majalisar ya gabatarwa dangane da binciken da majalisar take son kan mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu na II.
Yayin zaman majalisar dai ta kawunan ‘yan majalisar ya rabu gida biyu da masu goyan bayan kudirn da akasin haka kasancewar an hango wasu daga cikin ‘yan majalisar suna Dambatawa dauke sandar majalisar, kafin daga bisani a karbo ta.
Wakiliyar mu Khadija Ishaq Muhammad ta rawaito cewar, yanzu haka dai majalisar ta tafi hutun mintuna talatin, sai dai kuma a na tsaka da haka sai wasu mambobin majalisar na bangaren adawa suka karya karafan da ake dora sandar majalisar.
You must be logged in to post a comment Login