Coronavirus
Da dumi-dumi: Daukacin masu Corona sun warke a Jigawa
Hukumomin Lafiya a Jihar Jigawa sun tabbatar da cewa babu sauran mai cutar Corona a Jihar.
Kwamishinan Lafiya kuma shugaban kwamatin dakile yaduwar cutar na Jihar Jigawa Dr. Abba Zakari Umar ne ya tabbatar da haka, ya yin zantawar sa da Freedom Redio a ranar Litinin.
Dr. Abba ya kara da cewa sama da makwanni biyu ke nan ba a samu wanda ya kamu da cutar ba illa mutum guda, wadda shima ba dan Jihar bane, kuma tuni ya koma Jihar sa don cigaba da karbar kulawar Likitoci.
Haka kuma kwamishinan yace yanzu haka cibiyoyin killace masu cutar da gwamnatin jihar Jigawa ta ware babu kowa a ciki yanzu haka, wadda yace hakan ba karamar nasara jihar ta samu ba.
Labarai masu alaka:
Covid-19: Ma’aikata za su koma bakin aiki a Jigawa
Mai Corona daya ne ya rage a jihar Jigawa
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito Dr. Abba na cewa al’ummar Jihar Jigawa sun bada hadin kai matuka gaya, wajen yaki da wannan cuta ta COVID-19 ta hanyar bada rahoton duk wanda suka ga nada alamun cutar.
Kazalika, ya bukaci al’umma suci gaba da bin dokoki dakile yaduwar cutar ya yin da suke rayuwa da cutar, wanda yace muddin mutane suka kiyaye za su yi rayuwa cikin salama, kuma da sannu komai zai koma dai-dai.
You must be logged in to post a comment Login