KannyWood
Da gaske Adam Zango ya dauki nauyin karatun dalibai?
Mahukunta a makarantar Farfesa Ango Abdullahi dake Zaria, sun tabbatar da cewa jarumin fina-finan Hausa Adam A. Zango ya dauki nauyin karatun dalibai marayu guda 101 a makarantar.
Yayin tattaunawar da Freedom Radio tayi da shugaban makarantar Mallam Hamza Jibril ya tabbatar mana da cewa sun samu takarda daga dauke da bayanan cewa Adam Zango yana son zai dauki nauyin karatun dalibai har guda 101, kuma bayan da suka gama tattaunawa tuni Adam Zangon ya biya kudin tun a makon da ya gabata.
Dangane da daliban da za’a dauki nauyin karatun nas Mallam Hamza ya bayyana cewa Adam Zango ya baiwa masarautar Zazzau gurbin mutane 50 sai jam’iyyar APC aka bata gurbin mutane 31 sai kuma jam’iyyar PDP da aka baiwa mutane 20.
Dukkan su bisa sharadin zasu kawo dalibai marayu, ko talakawa da iyayen su basu da ikon biya musu kudin makaranta.
Haka zalika Mallam Hamza ya karyata dukkan rahotonnin dake yawo a soshiyal midiya na cewa batun daukar nauyin karya ne ba gaskiya bane.
Duk kokarin da Freedom Radio tayi na jin ta bakin jarumin Adam A. Zango amma abin ya ci tura, sai dai wani makusancinsa ya tabbatar mana da cewa Adamun ya dauki nauyin wadannan dalibai.
Tun a yammacin jiya ne dai labaran yake ta yawo a sohiyal midiya na cewa a damun ya dauki nauyin karatun daliban inda wasu ke ta gasgata labarin wasu kuma ke karyatawa.
RUBUTU MAI ALAKA:
Na taba yin soyayya da Maryam Yahaya a baya –Mai Shadda
Abinda ya sanya ba zan iya auren Yawale a zahiri ba -Rayya
Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?
Kun san dalilan da suka sanya aka garkame Sadiya Haruna a gidan yari?