Labarai
Dalibai 2,700 a Jigawa sun rubuta jarabawar neman gurbin tafiya karatun Likita
Dalibai 2,700 ne suka zana jarabawar farko ta neman samun damar tafiya karatun zama likita kasashen Ketare , wadda gwamnatin jihar Jigawa ta shirya don zabar dalibai 60 daga ciki.
Hakan na zuwa ne bisa karkashin daukar nauyin karatun su zuwa kasar Sin (China ) a karkashin shirin da Gwamnatin jihar ta bullo dashi ga yayan Marasa galihu.
Labarai masu Alaka.
Kungiyar KASSOSA ta gudanar da taronta na shekara a jihar Jigawa
Ma’aikatan lafiya sun kamu da Corona a Jigawa
Kwamishinan Lafiyar jihar Jigawa Dr. Abba Zakari ne ya bayyana haka ga manema Labarai a Dutse, ya yin gudanar da jarabawar da daliban suka yi, a makarantar Koyon Mulki da kasuwanci dake Dutse wato Jigawa State Polytechnic, a ranar litinin din nan.
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo daga Dutsen jihar Jigawa , ya ruwaito cewar bayan tantance wanda suka samu Nasara , dalibai 60 ake sa ran zasu ci moriyar tallafin Karatun .
You must be logged in to post a comment Login