Labarai
Dalilan da ya sanya Ganduje ya soke tsarin sabon mafi karancin albashi
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya soke tsohon mafi karancin albashi na Naira dubu 30 da ake biyan ma’aikatan jihar Kano.
Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya dena biyan ma’aikatan da sabon mafi karancin albashin ne na Naira dubu 30 sabo matsin tattalin arziki ya yin da za’a koma kan tsohon tsarin na Naira dubu 18.
Da yake ganawa da manema labarai maitaimaka wa gwamnan kan kafafan sadarwa Salisu Tanko Yakasai ya bayyana hakan a yau Laraba.
Salisu Tanko Yakasai ya ce Ganduje ya dauki matakin ne biyo bayan tabarbarewar tattalin arziki da ake fuskanta sakamakon cutar Corona da ta addabi duniya.
Akan haka ne gwmnatin Kano ta ce ba zata iya cigaba da biyan albashin ma’aikatan ba da sabon tsarin albashin na Naira dubu 30 ba.
Idan za’a iya tunawa a watan Afirilun bara ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya hannu kan dokar sabon mafi karancin albashin, biyo bayan matsin lamba da kungiyar kwadago ta yi wa gwamnatin tarraya aka kuma tsaya akan Naira dubu 30.
Ya yin da gwamnatin Kano ta cimma matsaya da ma’aikata wajen biyan sabon mafi karancin albashi bayan da gwamnatocin jihohi suka fara aiwatar da biyan sabon albashin.
You must be logged in to post a comment Login