Labaran Wasanni
Dan wasa Son, zai karbi horon aikin Soji a South Korea
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Totenham Hotspurs Son Min Hueng, zai karbi horon aikin Soji, da Kasar sa ta South Korea, ke sakawa tilas akan kowanne dan kasar.
Mai shekaru 27, Son wanda a baya aka dage masa karbar atisayen a baya sakamakon kasancewar sa dan kwallon kafa da yake taka leda a nahiyar Turai, da kuma jagorantar kasar sa da yayi wajen samun lambar zinare, a gasar wasannin kasashen nahiyar Asiya, yanzu haka zai yi mako hudu na karbar horon kasancewar ya dawo gida sakamakon dage gasar Firimiyar kasar Ingila da kayi akan cutar Corona.
Dan wasan wanda rabon sa da buga wasa tun watan Fabrairu, sakamakon karyewa da yayi a hannu a wasan da kungiyar sa ta fafata da Aston Villa, ana sa ran zai dawo wasa a watan Mayu, sai dai yanzu haka duk da killace kansa da dan wasan ya yi a kasar tashi, zai amfani da wannan tsaiko don yin horon na aikin Sojin kasar tashi.
Labarai masu alaka.
Da Dumi-Dumi: Mahaifiyar Guardiola ta rasu sakamakon Covid-19
Yanzu -yanzu an dage gasar wasanni ta kasa saboda barazanar Corona
A sanarwar da kungiyar sa ta Totenham ta fitar, ta ce likitocin kungiyar na tuntubar dan wasan akai- akai don jin hali da yake ciki, tare da tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya don aiwatar da wannan atisaye da ya zama wajibi.
A na sa ran cewar dan wasa Son, zai komo Ingila a watan Mayu, bayan kammala karbar horon tare da shiga cikin tawagar kungiyar tashi ta Totenham.
You must be logged in to post a comment Login