Labaran Wasanni
Dele Alli zai fuskanci hukunci kan cutar Corona
Daga kasar Ingila hukumar shirya gasar Firimiyar kasar ta Ingila ta dakatar da dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Dele Alli wasa Daya bisa yada wani labari da yai a kafar sadarwa ta Internet.
Labarin na da alaka kan yadda annobar Corona ke yaduwa a fadin Duniya a wannan lokacin.
Hukumar ta ce Alli, ya fitar da wani faidai Bidiyo ne a watan February daya gabata dake nuna barkonci kan annobar ta Corona.
Haka kuma hukumar ta ci tarar dan wasan kudin da ya kai £50,000 tare da umartar sa dayaje yai karatu na musamman kan yadda ya kamata ya rinka sanya abubuwa a kafar sadarwa ta Internet.
Dale Alli na daya daga cikin ‘yan wasan da tauraruwar su ke haskawa a kungiyar ta Tottenham, da kasar sa da yakewa wasa ta England bisa irin kwazon da yake nunawa.
You must be logged in to post a comment Login