Ƙetare
Dokar Tilastawa mutane nuna shaidar rigakafin Korona ta soma aiki a Tunisia
Gwamnatin Tunisia ta ce daga yanzu ya zama dole dukkanin ‘yan ƙasar da kuma baƙi su nuna shaidar karbar allurar rigakafin cutar COVID-19 kafin shiga wuraren tarukan jama’a.
Karkashin dokar da shugaba Kais Saed ya sanar a Juma’ar da ta gabata, ana bukatar manyan jami’ai da sauran ma’aikata su nuna katin dake tabbatar da sun yi allurar rigakafin cutar Korona.
Wannan ne zai ba su damar gudanar da ayyukansu a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu.
Har ila yau, za a bukaci shaidar rigakafin kafin shiga gidajen abinci, otal-otal da wuraren yawon shakatawa.
Sabuwar ta Tunisia ta kuma nuna cewar za a dakatar da ma’aikatan da ba su yi allurar rigakafi ba a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu, har sai sun gabatar da shaidar.
rfi
You must be logged in to post a comment Login