Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

ECOWAS na shirin kashe Dala miliyan 25 don yaƙi da ta’adda ci a Nijeriya da Nijar

Published

on

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta ware kimanin Dalar Amurka miliyan 25 domin yaƙi da ta’addanci a ƙasashen Nijeriya da Nijar da Mali da kuma Burkina na Faso.

Ecowas ta tsara kashe kuɗin ne a bana kamar yadda Kwamashinar Raya Al’umma ta Ecowas Farfesa Fatou Sarr ta bayyana a shalkwatar ƙungiyar da ke Abuja ranar Juma’a.

Ta ce, an ware miliyan huɗu daga cikin kuɗin don ayyukan agaji musamman ga mutanen da bala’o’i suka shafa.

BBC ta ruwaito cewa, jami’ar ta kuma ce, “Ecowas ta kuma ware dala miliyan ɗaya da zimmar daidaita rayuwar mutanen da ta’addanci ya shafa, kamar ƴan gudun hijira da kuma waɗanda aka ji wa rauni.”

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!