Ƙetare
ECOWAS zata gudanar da taron gaggawa kan juyin mulki
Shugabanin kungiyar kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko kuma CEDEAO, za su gudanar da wani taron gaggawa a gobe Lahadi game da juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.
Shugaban kasar nan,kuma sabon shugaban kungiyar Bola Ahmed Tinubu,shine zai jagoranci zaman wanda za a gudanar a babban birnin tarrayayyar Abuja.
Cikin wata sanarwa, Shugaba Tinubu ya yi Alla-wadai da juyin mulkin, inda kuma ya yi wa al’ummomin kasashen waje alkawarin cewa zai yi duk mai yiwuwa domin kare dimokuradiyya da kuma tabbatar da dorewar kyakkyawan shugabanci a yankin.
Shugaba Tinubu ya kuma yi fatan wannan taron na su zai samar da matsaya guda wadda za ta ba da damar mayar da Jamhuriyar Nijar kan turbar dimokuradiyya
You must be logged in to post a comment Login