Labarai
EFCC ta cafke Rochas Okorocha
Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta cafke tsohon Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, jami’an hukumar sun cafke Okorocha ne da yammacin jiya Talata a Abuja.
Ana zargin tsohon Gwamnan wanda ya mulki jihar Imo daga shekarar 2011 zuwa 2019 da yin sama da faɗi da dukiyar al’umma, zargin da ya musanta.
A baya dai Gwamnatin jihar ta yanzu ƙarƙashin Gwamna Hope Uzodinma ta ƙwace wasu kadarori da ake zargin matar Ukorocha ta mallaka ba bisa ƙa’ida ba.
Ko a cikin watan Fabrairun da ya gabata tsohon Gwamnan ya bayyana a gaban ƴan sanda bayan wani rikici da ya shiga da jami’an Gwamnati mai ci, game da kadarorin matarsa da aka ƙwace, kafin daga bisani su sallame shi.
Wannan dai shi ne, babban kamun da hukumar yaƙi da rashawa ta yi, tun bayan hawan sabon shugaban ta Abdurrashid Bawa.
You must be logged in to post a comment Login