Labaran Wasanni
Enyimba ta dauki Finidi George a matsayin sabon mai horarwar ta

Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ta nada tsohon Dan wasan Najeriya Finidi George a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasan ta.
Finidi George ya sakawa kungiyar kwantaragin shekaru 2 ne bayan da ya karbi mai horar da kungiyar ta Enyimba da kwantaragin shi ya kare a watan Augustan shekarar 2021 Fatai
Osho.
Ahmad Musa zai iya yiwa Najeriya wasanni 140-Vincent Enyeama
George ya buga wasa a kungiyar Ajax dake kasar Holland inda ya daukar mata kofin zakaru na Turai wato Champion league a shekarar 1995 sannan ya yi wasa a kungiyar Real Betis da Mallorca dake kasar Spain.
George, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles wasanni 62.
Ya kuma daukarwa Najeriya kofin Afrika a shekarar 1994 sannan ya wakilci kasar nan a gasar cin kofin Duniya a shekarar 1994 da 1998.
You must be logged in to post a comment Login