Connect with us

KannyWood

Kalubale na na farko a masana’antar Kanny Wood shine kin amincewar Iyaye–Rukayya Dawayya

Published

on

Fitacciyar jaruma kuma mai daukar nauyin fina-finai wato Rukayya Umar Santa wadda aka fi sani da Dawayya ta bayyana cewa ta samu nasarori da dama a zamanta a masana’antar Kannywood.

Yayin wata tattaunawa da tayi da Freedom Radio ta bayyana cewa ta samu nasarori da dama a rayuwarta cikin sama da shekaru goma sha biyar da ta shafe a masana’antar.

Dawayya ta ce babbar kalubalen data fuskanta kafin ta shigo masana’antar shi ne rashin yarjewar iyayen ta, domin kuwa a farko sun nuna rashin amincewar su kafin daga bisani  suka amince.

Ta kara da cewa ta samu cigaba matuka tun sanda  tazo masana’antar Kannywood a farko.

A karshe jaruma Dawayya ta mika sakon godiya ga masoyanta bisa addu’oi da goyan bayansu gareta.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!