Labaran Wasanni
Kasar Guinea bata shirya fafatawa da Nigeria ba
Hukumar Kwallon kafa ta kasar Guinea , wato Federation Guinean de Football (FGF) ta roki hukumar Kwallon kafa ta kasa Nigeria Football Federation (NFF), da ta canja ranar wasan da kungiyoyin kasar guda biyu na mata ‘yan kasa da shekaru 17, zasu fafata na cancantar shiga gasar cin kofin duniya zagaye na biyu da zai gudana tsakanin kasashen.
Hukumar Kwallon kafa ta Guinea, sun bukaci a dage wasan da akayi niyyar fafata shi a karshen makon nan ,da Karin mako daya a gaba.
Rokon a canja ranar wasan ya biyo bayan , zaben da za a gudanar a kasar ta Guinea, na yan majalisun kasar a ranar da za’a buga wasan , ran 29, ga watan Fabrairun da muke ciki.
A ta bakin kakakin hukumar Kwallon kafa ta kasa Ademola Olajire, a wata takarda da ya sawa hannu, ta tabbatar da amincewar hukumar kwallon kafa ta kasa NFF, inda yanzu haka za a yi wasan farko ne a can kasar Guinea, ranar Asabar din 7 ga watan Maris , wanda hakan ya tabbatar da mako daya kacal tsakanin wasan farko a can kasar ta Guinea da kuma wasa na biyu da za fafata a filin wasa na ( Agege dake Ikko wato Lagos).
Rahoto : Nazari kan wasanni na gida tana ketare
Tsohon mai horas da Kano Pillars ya rasu
Magoya bayan Kano Pillars na kira da a kori mai horar da ‘yan wasan kungiyar
Zuwa yanzu haka dai ana dakon amincewar hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka wato Confederation of African Football (CAF), don sanin makomar wasan.
Rahoto: Daga Aminu Halilu Tudun wada
You must be logged in to post a comment Login