KannyWood
Fim din ‘yan Shi’a : Yakubu Muhammed ya nemi afuwa
Fitaccen jarumin nan na masana’antar Kannywood Yakubu Muhammed ya ce a shirye ya ke ya biya kudin karya yarjejeniya da masu shirya fim din mai taken: ‘‘fatal Arrogance’’, matukar su ka amince za su cire bangaren da ya fito a cikin fim din.
A wani zantawa da gidan rediyo BBC Yakubu Muhammed ya ce yayi matukar nadama da ya amince ya fito a cikin fim din.
Ya ce tuni ya sanar da mai shirya fim din cewa ya cire bangaren da ya fito a ciki, kuma a shirye yake ya biya kudin karya ka’idar yarjejeniyar kwantitagi.
.
Yakubu Muhammed ya kuma ce sam kokadan bai san cewa wasu daga cikin sashe na fim din zai kasance kamar yadda ya gani daga bisani ba.
YaKUBU Muhammed dai ya fito sau shida a cikin fim din wanda kuma aka harbeshi har ya mutu.
Fim din da aka fara fitar da tallansa ya bayyana yadda rikici ya kaure tsakanin mabiya shi’a da sojoji a garin Zari’a da ke jihar Kaduna.
A cewar Yakubu Muhammed, tun farko labarin fim din bai ga inda ya ke da alamar cin zarafin addini ba, sai dai daga bisani yaga sabbin abubuwa wadanda basa ciki tun da fari.
You must be logged in to post a comment Login