Kaduna
FRSC ta kama masu karya dokokin tuki 262 a jihar Kaduna
Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC reshen jihar Kaduna ta ce ta gurfanar da wadanda suka karya dokokin tuki su akalla dari biyu da sittin da biyu a jihar, daga watan Janairu zuwa Agustan da ya gabata.
Babban kwamandan hukumar mai kula da shiyyar Kaduna Hafiz Muhammad ne ya bayyana hakan a yau.
Ya ce kotunan tafi-da-gidanka da hukumar ta samar guda bakwai sun kama mutane da laifuka da dama na karya ka’idojin hanya yayin da tuni ta sallami mutane goma sha tara.
Hafiz Muhammad ya kara da cewa mutane 75 aka kama da laifin rashin lasisin tuki yayin da mutana 48 kuma aka kama su da laifin dibar kaya fice da kima, sai mutane 42 da aka kama da laifin rashin madaurin direba wata seat belt.
Hka zalika mutane 39 sun aikata laifin gudun wuce sa’a sai kuma mutane 30 da suka aikata laifin yin tuki ba tare da abin goge gilashi yayin da ake ruwa.
Hafiz Muhammad ya ja hankalin direbobi da su guji karya dokokin tuki, inda ya bukaci fasinjoji da su kiyaye baiwa masu ababen hawa damar dibar kaya da suka wuce ka’ida.
You must be logged in to post a comment Login