Labarai
Ganduje ya ƙaddamar da ma’aikatar kula da harkokin addinin
Da safiyar yau Litinin ne gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ƙaddamar da ma’aikatar lura da al’amuran addinin musulunci a gidan Murtala dake nan Kano.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce, ma’aikatar zata riƙa kula da hukumomin da ke kula da harkokin addinin musulunci da kuma ɓangaren musuluntar da maguzawa tare da inganta mu’amala tsakanin musulmi da waɗanda ba musulmi ba don samun zaman lafiya.
Ya kuma ce, ma’aikatar zata riƙa shirya kasafin kuɗin da zata kashe a duk shekara.
Haka kuma, gwamnan ya buƙaci ma’aikatan dake ƙarƙashin ma’aikatar da su ci gaba da bada haɗin kai wajen tafiyar da ayyukan ma’aikatar yadda ya kamata.
Da yake jawabi a yayin ƙaddamar da ma’aikatar kwamishinan addinai na Kano, Muhammad Tahar Adam ya ce, wannan rana ce mai tarihi, kasancewar ba a taɓa samun ma’aikatar da gwamna ya je bude ta da kansa ba a cewarsa.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito kwamishinan na cewa yanzu haka shekarar ma’aikatar guda da fara aiki, kuma zata ɗora da ayyukan ta wajen tabbatar da ci gaban addinin musulunci a Kano.
You must be logged in to post a comment Login