Coronavirus
Ganduje ya gana da sarakuna kan Coronavirus
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gana da sarakunan gargajiyar biyar masu daraja ta daya na jihar kan annobar Covid-19.
Yayin ganawar da ta gudana a fadar gwamnatin Kano, Gwamna Ganduje ya nemi sarakunan da su rubanya ayyukan da sukeyi na wayar da kan al’umma kan cutar Corona.
Wakiliyarmu ta fadar gwamnatin Kano Zahra’u Nasir ta rawaito mana cewa gwamnan yace ya kamata sarakunan su jajirce wajen ilimantar da al’umma domin bin dokokin jami’an lafiya game da cutar da kuma zuwa wajen gwaji ga wanda aka gani da alamar cutar.
Da yake jawabi Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al’umma kan su dage wajen neman gafarar ubangiji tare da rika taimakawa marasa karfi a wannan yanayi da ake ciki.
Karin labarai:
Yadda cibiyar gwajin Corona ta Dangote ke aiki a Kano
Mutane 50 sun warke daga Corona a Kano
Har ila yau wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa mai baiwa ministan lafiya shawara akan cutar Corona a Kano Farfesa Abdussalam Nasidi ya ce cikin sati biyu da zuwansu Kano an samu nasara sai dai akwai bukatar karin gudummuwar sarakunan gargajiyar kan yakar cutar.
You must be logged in to post a comment Login