Labarai
Ganduje ya goyi bayan hukuncin kisa ga masu yin ɓatanci ga addini
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce, da zarar lokacin da aka ɗaukarwa wanda yayi ɓatanci ga Annabi Muhammad da aka yankewa hukuncin kisa a kwanakin baya ya cika, kuma bai ɗaukaka ƙara ba to babu shakka zai sanya hannu wajen zartar da hukuncin kisan da kotun ta yanke masa tun da farko.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a yammacin Alhamis ɗin nan, lokacin da ya gudanar da taron zantawa da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da malaman addini daga ɓangarori da dama, da lauyoyi tare da malaman jami’a da sauransu a fadar gwamnatin Kano dongane da hukuncin da aka yankewa wanda yayi ɓatanci ga annabi Muhammad (s.a.w).
Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da suyi hattara da irin wannan al’amari na zamani musamman ɓatanci ga shugaban halitta.
Kafin Gwamnan yayi bayanin sai dai da shugaban ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Kano Aminu Gadanya ya ce su dama tun da fari sun goyi bayan hukuncin na kisa da aka yankewa wanda yayi ɓatanci da akayi a kwanakin baya, sai dai doka ta baiwa wanda yayi ɓatancin damar daukaka ƙara.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa kafin jawabin na gwamnan Kano ɗin a yau sai da malamai daga ɓangarori da dama duk suka goya wa gwamnan baya don aiwatar da hukuncin domin haka addinin musulunci ya tanada ga wanda yayi ɓatancin ga annabi Muhammad SAW.
You must be logged in to post a comment Login