Labarai
Ganduje ya jagoranci musuluntar da mutane 138 a Kano
- Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci musuluntar da mutane dari da talatin da takwas.
- Ganduje yayi kira ga wadanda suka musuluntar da su yi kokari wajen bin dokokin Allah SWT.
- A hannu guda wadanda suka musuluntar sunce sun zabi addinin ne don samun nutsuwar gudanar da rayuwarsu.
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci musuluntar da mutane dari da talatin da takwas a jiya a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnati.
Da yake jawabi bayan musuluntar da mutanen maza da mata da suka fito daga karamar hukumar Sumaila gwamna Ganduje ya ja hankalinsu game da kulawa da Ibada tare da neman Ilimin addinin Musulinci.
Ganduje ya yi kira ga wadanda suka musuluntar da su yi kokari wajen bin dokokin Allah SWT, tare da riko da koyarwar addinin na islama.
Wasu daga cikin wadanda suka karbi shahadar ta muslinci sun bayyana cewa wa’azin da sukeji a unguwanninsu a cikin Azumi ya taka muhimmiyar rawa wajen jan hankalinsu su domin su shiga addinin.
A gefe guda kuma wasu daga cikin wadanda aka musuluntar din sun ce sun gano cewa ana samu nutsuwa da addinin musulunci, wanda hakan yasa suka amince su shiga domin su cigaba da gudanar da rayuwarsu akan tafarkin gaskiya da kuma tsari.
A yayin taron, an raba kayan sallah ga wadanda suka musulunta maza da mata tare da raba musu jari domin su dogara da kansu.
Rahoton: Abba Isah Muhammad
You must be logged in to post a comment Login