Labarai
Ganduje ya kaddamar da kwamitin kula da ayyukan Burtalai
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da babban kwamitin da zai rika kula da harkokin Burtalai a nan Kano.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin ne a yau wanda manajan daraktan hukumar bunkasa aikin noma da raya karkara na jihar Kano Ibrahim Sulaiman Dan’isle zai jagoranta ta wanda aka kaddamar a ofishin su.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Kuma kaddamar da rabon motoci da babura wanda yace gwamnati da masu taimaka mata sun samar da su ne ga manoma don rika amfani dasu don saukaka zirga-zirga
A yayin taron gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Kuma ce Kara da cewa dokar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta hana shigo da abinci daga waje ta taimakawa manoma wajen yin noma a kasar nan tare cin riba.
Gwamnnatin Kano ta shawarci manoma dasu kalli noma a matsayin riba
Yadda aka sami arangama tsakanin manoma da makiyaya a Jigawa
RIFAN za ta tallafawa manoman da ambaliyar ruwa ta shafa a Kano
A nasa bangaren manajan daraktan hukumar bunkasa noma da Raya karkara na Kano Ibrahim Sulaiman Dan’isle ya godewa gwamnatin Kano bisa ga samar da motoci da baburan zirga-zirga ga manoma.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa kwamitin harkar Burtalin Yana da wakilici daga wasu maaikatu a nan Kano tare da kuma Masaurautun Kano biyar.
You must be logged in to post a comment Login