Labaran Kano
Ganduje ya kafa kwamitin da zai sanya ido kan kafafen yada labarai
Gwamnatin jihar Kano ta amince da kafa wani kwamiti da zai rika sanya ido tare da tsaftace ayyukan kafafen yada labarai a jihar Kano.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan yau juma’a yayin zantawa da manema labarai kan abubuwan da aka tattauna a taron Majalisar zartarwa na wannan makon da aka gudanar a ranar talatar da ta gabata.
Malam Muhammad Garba ya ce sakataren gwamantin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ne ya gabatar da wata takarda da wasu mutane suka aiko inda suka nuna damuwarsu kan yadda ake cin zarafin mutane a wasu kafafen yada labarai a Kano wanda hakan ya saba da dokokin aikin jarida.
Masu korafin sun bukataci gwamnati ta dau matakan gaggawa don kare wannan matsala, kasancewar ana zubarwa da jihar Kano mutunci a idon duniya.
LABARAI MASU ALAKA DA WANNAN
Ganduje zai mayar da dajin Falgore wurin atisayen sojoji
Ganduje zai fara gurfanar da iyayen almajirai masu bara a gaban kotu
Uwar jam’iyyar APC ta taya Ganduje murnar samun nasara a kotun koli
A nan ne majalisar ta amince da kafa wani kwamitin na musamman don tsaftace harkokin kafafen yada labarai, inda aka na Kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba a matsayin shugaban kwamitin, sai kuma Farfesa Umaru Pate a matsayin mataimakin shugaba.
Wakiliyar mu ta fadar Gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta Ruwaito Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano malam Muhammad Garba ana bayyana cewa tuni gwamnati ta saki kudi domin fara gudanar wasu ayyuka wanda suka hada da aikin kare zaizayar kasa a gurare daban daban dake karamar hukumar Garko.
You must be logged in to post a comment Login