Coronavirus
Ganduje ya magantu kan sassauta dokar kulle a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta magantu kan sassauta dokar kulle a jihar da gwamnatin tarayya tayi.
A cikin wata sanarwa da Gwamnatin Kano fitar a daren Litinin dinnan ta ce kasuwanni da wuraren ibada zasu rika kasancewa ne ranakun Lahadi da Laraba da Jumu’a daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba ta kara da cewa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kira taro da shugabannin kasuwanni game da yadda za a kula da ka’idojin kariyar cutar Corona a kasuwannin
Sanarwar ta kuma kara da cewa ya zama lallai a tabbatar ana amfani da takunkumin rufe baki da hanci da kuma yawaita wanke hannaye a wuraren.
Sannan sanarwar ta ce duk da cewar makarantu zasu cigaba da kasancewa a rufe akwai bukatar dalibai su rika amfani da damar darussan da gwamnatin ta dau nauyi a kafafen yada labaran talabijin da rediyo.
You must be logged in to post a comment Login