Labaran Kano
Ganduje ya nada sabon shugaban hukumar tattara haraji ta Kano
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada Abdurrazak Datti Salihi a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kudaden haraji na cikin gida a Kano wato KIRS.
Nadin zai fara aiki ne nan take, yayin da Ganduje ke sake godewa Bala Muhammad wanda yake rike da ma’aikatu biyu a lokaci guda da suka hada da KASCO da KIRS a matsayin mukadashin ta.
Shi dai sabon shugaban hukumar tattara kudaden shiga na cikin gida yana da kwarewa a harkokin kudi da Akanta da kuma tattara kudaden haraji na fiye da shekaru 20 bayan da ya yi aiki a bangarori daban-daban na gwamnati da masu zaman kan su da suka hada da banki.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da sakataren yada labarai ga gwamnan Abba Anwar ya sanya wa hannu cewa, kafin nadin nashi ya rike mukamai daban-daban ciki har da darakta a ma’aikatar kudi ta jihar Kano.
Labarai masu alaka :
Majalisar dokoki ta bukaci Ganduje ya magance matsalar ruwa a Kano
Ganduje ya nada mai taimaka masa kan daukar hotuna
Ganduje ya aikewa majalisar dokoki sunayen mutum biyu – KANSIEC
A cewar, sanarwar gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi kira ga sabon shugaban da ya sadaukar da kan sa wajen gudanar da aiki don cigaban hukumar ta tattara kudaden haraji ta cikin gida da ma jihar Kano baki daya.
You must be logged in to post a comment Login