Labaran Kano
Ganduje : Za mu saka kafar wando daya da masu kin sanya Amawali
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata hada Kai da jamian tsaro domin shawo matsalar rashin sanya safar Baki da hanci da alumma basa dauka da muhimmaci.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a yau lokacin da yake gudanar da taron majalisar zartarwa da ake gudanarwar duk ranakun laraba aka kuma gudanar da shi a yau Talata.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kara da cewa hakika a nan Kano ana samun nasarar yakar Corona in akayi la’akari da yawan al’ummar da ake gwadawa wadanda ake samu da cutar basu da yawa adon haka ne ya yi kira ga al’umma wajen cigaba da bin kaidojin yakar ta.
Ya Kara da cewa kasancewar har yanzu al’umma basu son sanya safar ta baki da hanci ba adon hakane ma ya ce zasu tattauna da jamian tsaro da sauran masu fada aji don ganin yadda zaa shawo kan alamarin.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kuma ce cigaba da fadakar da al’umma kan bin dokokin masana dongane da kariyar Corona zai taimaka wajen kawar da ita gaba daya.
You must be logged in to post a comment Login