Labaran Kano
Ganduje : za’a rufe kan iyakokin jihar Kano COVID-19
Daga ranar Juma’a 27 ga Watan Maris din nan, da karfe 12 na dare ne za a rufe duk iyakokin shigowa jihar Kano, duk cikin kokarin ko-ta-kwana na gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje saboda neman tsari daga mummunar cutar nan ta CORONA VIRUS.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya fitar cewar, dukkan fasinjoji masu zuwa jihar ta bangaren zirga-zirga na cikin gida, ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano, ba za a bar su shiga cikin garin Kanon ba, sai dai su zauna a filin jirgin saman.
A cewar sanarwar hukumomin ‘Yan Sanda da na KAROTA da na Hisbah da sauransu za su sanya ido sosai wajen ganin an yi aiki da wannan umarni.
Sannan an umarci jama’a da su baiwa jami’ai hadin kai, da kuma bin shawarwarin jami’an kiwon lafiya don kare kai daga kamuwa daga cutar.
Kazalika ma’aikatan gwamnati da a ka ce kar su je aiki, an yi hakan ne domin su zauna a gidajensu saboda tsare kansu, da kuma jama’a su ma a na shawartarsu da su janye jikinsu daga kasuwanni, in dai ba bisa abinda ya zama dole ba.
Daga karshe sanarwar ta kara da cewar, da wanke hannu da sabulu da ruwa da kara tsaftar muhalli ya zama wajibi a lura da su, saboda lafiyar alumma da jihar nan da kasar nan gaba daya.
Sannan a na rokon jama’a da su ci gaba da yin addu’o’in neman sauki daga Allah Mahaliccinmu.
You must be logged in to post a comment Login