Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Garkuwa da mutane ta sanya mutanen Kano fargaba

Published

on

Matsalar satar mutane da neman kuɗin fansa, matsala ce da har yanzu aka kasa magancewa a sassan ƙasar nan.

A baya dai ba kasafai aka fiya samun rahotonnin garkuwa da mutane a jihar Kano ba, saɓanin yanzu da ake samunsa tsilli-tsilli.

Rahotannin garkuwa da mutane da ake samu a Kano

Cikin wannan makon da muke ciki ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗan uwa ministan noma na ƙasa a ƙaramar hukumar Gabasawa.

A watan Oktoban da ya gabata kuwa, ƴan bindiga sun yi garkuwa da matar dagacin garin Tsara a ƙaramar hukumar Rogo.

Daga baya suka sako ta, bayan an biya fansar kudi har miliyan biyu.

Kuma duk da haka, suka riƙe ɗan uwanta da ya je kai kuɗin fansar, tare da jikkata wakilin dagaci da yayi masa rakiya.

Yan sanda masu yaki da garkuwa da mutane

A watan Janairun wannan shekara ƴan ta’adda sun yi garkuwa da dagacin garin Karshi a ƙaramar hukumar ta Rogo.

A watan Augustan da ya gabata kuwa ƴan bindigar sun tsare hanyar dajin Falgore inda suka kutsa da mutane cikin daji.

Sannan su ka jikkata wasu, ciki har da kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Doguwa.

Cikin watan Yuli na wannan shekara ta 2020 ma, masu garkuwa da mutane sun kutsa gidan ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɗanbatta, wato Murtala Musa Kore.

Har ma suka yi awon gaba da ƴarsa mai suna Juwairiyya.

A wancan lokaci, ɗan majalisar ya koka kan matsalar tsaro, har ma ya ce, mutane su tsare kansu domin abin ya wuce yadda ake tunani.

Idan zaku iya tunawa a watan Yulin shekarar 2019, ƴan sanda suka kuɓutar da magajin garin Daura.

A unguwar Gwazaye da ke nan Kano bayan da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi.

Magajin Garin Daura lokacin da aka kubutar da shi daga masu garkuwa da mutane a Kano.

Haka ma a watan Maris na shekarar 2019 wasu ƴan bindiga sun kutso har cikin birnin Kano inda suka hallaka mutane biyu a daidai gadar Dangi.

Suka kuma yi awon gaba da wani ɗan ƙasar Lebanon cikin ma’aikatan da ke aikin gina gadar.

Garkuwa tare da hallaka ƙananan yara a Kano

An samu rahotannin satar ƙananan yara da garkuwa da su.

Alal misali ko a makon da ya gabata rundunar ƴan sandan Kano ta cafke wani matashi da yayi garkuwa da ƙaramar yarinya mai shekara 8, a ƙaramar hukumar Gabasawa.

Ya nemi a biya shi fansar N500,000 kuma bayan ya karɓi kuɗin ne sai ya hallaka ta.

Makamanciyar wannan ma ta faru a watan Disamba na shekarar 2019 inda wani matashi yayi awon gaba da ɗan ƴar uwarsa.

Ya kuma nemi a biya shi fansar N300,000, daga bisani kuma ya hallaka yaron tare da jefar da shi a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Minjibir.

 

A watan Yuli na shekarar 2019 ma an zargi wata mata da yin garkuwa da ƙaramar yarinya.

Ita ma daga-bisani ta jefa ta a wata rijiya da ke unguwar Tukuntawa.

Garkuwa da mutane ta addabi yankin Falgore

A yankin Falgore dai al’ummar yankin sun jima suna kokawa da matsalar rashin tsaro.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, ba sa iya samun nutsuwa sakamakon fargabar da suke ciki game da ƴan bindiga.

Hukumomi dai sun samar da sansanin soji da na ƴan sanda a dajin, amma duk da haka wasu na cewa har yanzu ba ta sauya zani ba.

Kwamishinan yan sandan Kano Habu Ahmed Sani lokacin da ya ziyarci dajin Falgore.

Me masana tsaro ke cewa?

Masana kan al’amuran da suka shafi tsaro na cewa rashin ɗaukar matakin da ya dace tun matsalar na ƙarama shi ne abin da ke kara ta’azzarar ta.

Barista Audu Bulama Bukarti mai sharhi ne kan al’amuran tsaro.

Ya ce, akwai buƙatar gwamnati ta sake nazari na tsanake domin yaki da wannan matsala.

Bulama ya ce “Akwai abin tsoro a ciki, kuma matuƙar gwamnati ta ci gaba da jan ƙafa, da tsayawa iya maganganu a rediyo to abin zai ci gaba da yaɗuwa”.

Barista Audu Bulama Bukarti mai sharhi kan tsaro.

Me ya kamata al’umma su riƙa yi a wannan lokaci?

Barista Bulama ya ce, “Mu guji bin hanyoyin da muka san an taɓa samun wannan matsala, idan kuma zamu bi to mubi ido na ganin ido”.

“Mu dinga kula da waɗanda mu ke zaune da su saboda wasu da aka sace a baya, an gano da haɗin bakin na kusa da su”.

“Sannan mu dinga komawa gida da wuri, lallai mu tabbatar bama bin lunguna”.

Bulama ya ci gaba da cewa, “Tilas sai mun dage da addu’o’i sannan ita ma gwamnati ta yi abin da ya dace”.

Me jami’an tsaro ke cewa a kai?

A wani jawabi da kwamishinan ƴan sandan Kano Habu Ahmed Sani yayi ya ce, su na samun nasara matuƙa a yaƙi da masu garkuwa da mutane.

Har ma sun cafke masu garkuwa da mutane sama 100 cikin shekara guda.

Me gwamnatin Kano ta ce a kai?

Gwamatin Kano ta ce, lamarin abu ne da ke damunta kuma tana jajantawa waɗanda lamarin ya shafa.

Mai taimakawa gwamnan Kano kan yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai ya ce, gwamati ba ta bacci saboda matsalar.

Ya ce, gwamna Ganduje na roƙon jama’a kan su riƙa bada haɗin kai wajen yaƙi da masu garkuwa da mutanen.

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ministan tsaro na kasa Gen. Bashir Salihi Magashi lokacin aza harsashin ginin filin atisayen sojoji a Falgore a watan Fabrairun shekarar 2020.

Meye hukuncin masu garkuwa da mutane a Kano

A watan Nuwamban shekarar 2019 gwamna Abdullahi Ganduje ya ce, ya amince da hukuncin kisa a kan duk wanda aka samu da yin garkuwa tare da hallaka mutum a Kano.

A shekarar 2016 ma majalisar dokokin jihar Kano ta taɓa sabinta dokar kisa ga masu garkuwa da kashe mutane.

Dokar dai ta na wani ɓangare na dokar penal code da gwamnatin lardin arewa ta samar a shekarar 1963.

Wasu dai na ganin cewa sai an yi haɗaka tsakanin jihohi maƙota domin ganin an kawo karshen matsalar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!