Labarai
Gina Jami’a da kungiyar Izala zata yi zai cike gibi ilimi a yankin Arewa – Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce aza harsashin gina Jami’a mai zaman kanta da kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ke kokarin yi a garin Hadeja zai taimaka wajen cike gibin rashin Jami’o’i a yankin Arewa.
Gwamna Tambuwal ya bayyana hakan ne da yammacin jiya lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin Jihar Kano, jim kadan bayan dawowarsu daga Hadejia tare da gwamnan Kano.
Tambuwal ya kara da cewa idan aka yi la’akari da yadda dalibai da dama ke gaza samun guraben shiga Jami’a sakamakon karancin Jami’o’in da ake da su a yankin Arewa maso yammacin kasar nan, to babu shakka Jami’ar za ta taimaka wajen cike gurbin matasa dake neman shiga Jami’a.
Amfani da kafafen sada zumunta a gurgunce na dakile ilimin matasa – Ganduje
Samar da dangantaka mai kyau a jami’o’i zai kawo cigaba – Adamu Adamu
Hukumar NYSC ta gargadi Hukumomin Jami’o’in Najeriya
Aminu Waziri Tambuwal ya kara da cewa tuni aka samar da kwamitoci biyu a Jihar Sokoto da ke aiki a kan yawan barnar ruwan da aka samu da ta shafi al’umma musamman a gonaki da dabbobi da kuma gidajen al’umma.
Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa gwamnan na Sokoto ya ce nan ba da dadewa ba za a gabatar da kwarya-kwaryar kasafin kudi a majalisar jihar don samun hanyoyin gyara matsalolin da taimakon wadanda ruwan ya yi wa barna.
You must be logged in to post a comment Login