Labarai
Gina Ruga ta zamani zai magance matsalolin Fulani -Munir Ahmad Gwarzo
Gwamnatin jihar Kano ta nuna kwarin guyiwar ta wajen magance matsalolin Fulani Makiyaya da Manoma a fadin jihar Kano, idan aka kammala aikin gina Ruga ta zamani.
Manajan Daraktan Hukumar kula da albarkatun ruwa da gine gine ta jihar Kano (WRECA) Alhaji Munir Ahmad Gwarzo ne ya bayyana hakan, yayin tattaunawa da wakilin Freedom Radio Umar Idris Shuaibu.
Ya ce tuni shiri ya yi nisa wajen samar da kasuwar sayar da tsaftataccen albarkatun Nono a kusuwannin jihar Kano da kuma samar da Ruga ta zamani a Dajin Dan Soshiya dake karamar hukumar Kiru, karkashin jagorancin kwamitin gina Ruga ta zamani da Gwamnatin jihar ta kafa a baya, wanda Manajan Daraktan hukumar kula da dukiyoyi da zuba jari na jihar Kano (KSIP) Dakta Jibrilla Muhammad ke jagoranta da hadin gwiwar kungiyoyin ci gaban Fulani na Jowrows da Fuldan da kuma Miyetti Allah.
Alhaji Munir Ahmad Gwarzo wanda mamba ne a kwamitin, ya ce shakka babu aikin gina Rugar yazo dai-dai da zamani, don baiwa rukunin wannan al’umma ta Fulani damar yin rayuwar su kamar kowa, da kuma amfanar abubuwan da suke samarwa daga shanun su na Nono da Nama don bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.
Rahotanni na nuni da cewa, wannan na zuwa ne, biyo bayan rikice-rikice da ake ci gaba da samu tsakanin Fulani Makiyaya da wasu al’ummar sassan kasar nan daban-daban.
Alhaji Munir Ahmad Gwarzo ya ce, aikin gina Ruga irin ta zamani zai kunshi samar da Makiyayu mai fadin gaske cikin dajin na Dan Soshiya, da kuma isassun mashayun ruwa ga dabbobin su dama famfuna na mutane, da hakan zai zama mai dorewa kasancewar aikin samar da Dam na ruwa yayi nisa cikin dajin.
You must be logged in to post a comment Login