Labarai
GSS ‘Yar Gaya ta baiwa dalibanta bita ta musamman
Makarantar ‘yan mata ta GSS ‘Yar Gaya dake karamar hukumar Dawakin Kudu a nan Kano, ta gabatar da wani taron bita na musamman ga dalibanta a yau Litinin.
Taron bitar wanda aka shirya domin wayar da kan daliban musamman kan yadda zasu rika gudanar da al’amuran su a lokacin hutu, sakamakon hutun karatu na mako guda da suka samu a makarantar.
Tunda farko a jawabinta shugabar makarantar Hajiya Uwani Ahmad Balarabe ta ja hankalin shuwagabannin makarantu dasu rika shiryawa daliban su bita don wayar da kan daliban su da kuma sanin halin da daliban ke ciki.
Hajiya Uwani ta kara da cewa daliban suna bukatar a ware musu lokacin da zasu rika yin wasanni da gasa, da kuma kacici kacici har ma da wasan kwaikwaiyo.
Karin labarai:
Gwamnati ta dakatar da wasu daliban Sakandire a Kano
Daliban Sakandire sun yi zanga-zanga a Bauchi
Har ila yau, Hajiya Uwani ta ce akwai bukatar shuwagabannin makarantu su rika hada kan dalibansu wajen gabatar da wasu wasanni, tana mai cewa hakan wata hanya ce ta janyo daliban a jika, kuma hakan zai kara musu kaifin kwakwalwa.
A nasa jawabin shugaban kungiyar iyayen yara na makarantar, Alhaji Umaru Nata Gandu ya ce yana da matukar muhummanci iyayen yara su rika ziyartar makarantun domin sanin halin da yaransu ke ciki.
Wasu daga cikin daliban sun bayyana farin cikin su da wannan rana, inda suka ce sun karu matuka da jawaban da akayi a yayin taron.
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa iyayen yara da shuwagabannin unguwa da dama ne suka halarci taron.
You must be logged in to post a comment Login