Connect with us

Labarai

Gwamantin tarayya ta koka bisa karuwar safarar mutane

Published

on

Gwamnatin tarayya, ta bayyana damuwa bisa yadda masu safarar mutane ke kara yawaita musamman ma ta hanyar kafar Internet da kuma suke amfani da hanyar wajen hilatar ‘yan kasar nan.

Atoni Janar kuma Ministan shari’a Lateef Fagbemi SAN, ne ya bayyana hakan jiya Laraba a birnin tarayya Abuja yayin da ya ke jawabi a taron masu ruwa da tsaki a fannin dakile matsalar safarar bil’adama karo na 27.

Haka kuma, ministan shari’an ya bukaci a dauki kwararan matakan shari’a kan wannan batu tare da tare da bukatar kwamishinonin harkokin mata na jihohin kasar nan 36 da su samar da sabbin tsare-tsaren magance, safarar mutane.

A nata bangaren, Darakta Janar ta hukumar dakile safarra bil’adama ta kasa NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta bayyana cewa, sun kubutar da fiye da mutane 7,000 da aka yi safarar su a tsakanin shekarun 2022 zuwa 2024.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!