Labarai
Gwamnati jihar Kano ta ce yara sama da miliyan biyu ne ke zuwa makaranta a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce akalla sama da yara miliyan daya da dubu dari tara ne ‘yan aji daya zuwa uku ke halartar makaranta a fadin jihar a wannan lokaci.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sunusi Kiru ne ya bayyana hakan, yayin zantawa da manema labarai, jim kadan bayan da ya mika ragamar jagorancin ma’aikatar na wucin gadi ga wani yaro mai suna Azzubair Bashir, a wani bangare na bikin ranar yara ta duniya da ke gudana a yau.
Ya ce an samu wannan nasara ne biyo bayan fara shirin karatu kyauta kuma dole da gwamnatin jihar ta kaddamar a shekarun baya.
A cewar kwamishinan, a kowacce shekara gwamnatin jihar Kano tana kashe naira biliyan uku wajen gina sababbin azuzuwa da kuma gyaran wadanda suka lalace a fadin jihar baki daya.
Labarai masu alaka:
Gwamnatin Kano ta bada umarnin komawar sauran dalibai makaranta
Gwamnatin Kano zata kashe miliyan 200 don farfado da madatsar Ruwa ta Watari
Tun farko da ya ke jawabi, babban jami’in asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF anan Kano, Mr. Samuel Kalu ya ce sun shirya taron ne don nunawa yara makamar aikin gwamnati.
Mr. Samuel Kalu wanda ya sami wakilcin jami’ar da ke kula da yara a asusun Fatima Adamu ta ce hakan wata hanya ce ta karfafawa yaran gwiwa.
Wakilin mu Abdullahi Isah ya ruwaito cewa, asusun na UNICEF ne ya shirya taron, inda yaran da aka zabosu daga wasu makarantun gwamnati anan Kano, su ka karbi ragamar jagorancin ma’aikatun ilimi da na mata na dan wani lokaci daga wajen kwamishinonin.
You must be logged in to post a comment Login