Jigawa
Gwamnatin jigawa na yi wa ma’aikata rijista a shirin asusun kiwon lafiya

Gwamnatin jihar Jigawa, ta fara yi wa ma’aikatan jihar rijistar shirin Asusun kiwon Lafiya bayan sanya hannu kan dokar shirin da gwamnan jihar Alhaji Muhd Badaru Abubakar ya yi, tun a bara.
Babban Sakataran zartarwar hukumar asusun kiwon Lafiya ta jihar Jigawa Dr. Nura Ibrahim Salisu ne ya bayyana haka ga manema labarai, jim kadan bayan fara yin aikin rijistar a gidan Gwamnatin jihar Jigawa.
Ku saurari wakilinmu daga Dutsen Jihar Jigawa Muhd Aminu Umar Shuwajo a cikin jerin labaru na nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login