Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kaduna ta sanya ranar karshe ta karbar kudin aikin Hajjin badi

Published

on

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana ranar 24 ga watannan da mu ke ciki a matsayin ranar karshe da maniyyatan jihar za su kammala biyan kudin aikin Hajjin badi.

 

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Ibrahim Adamu Datti, ya fitar ga manema labarai.

 

Hukumar ta ce an sanya karfe goma sha biyu na rana a matsayin lokacin da wa’adin zai cika.

 

Sanarwar ta kuma gargadi maniyyatan da ba su kammala biyan kudin ba kafin lokacin cewa za su iya rasa gurabensu na aikin Hajjin 2027.

 

Ya ce tun da farko hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON, ta bai wa jihar wa’adin tura kudaden zuwa 2 ga Disamba, sai dai daga baya aka matsar da wa’adin zuwa ranar 24 ga Satumbar wannan shekarar.

 

Hukumar ta bukaci maniyyatan da su gaggauta kammala biyan kudaden kafin wa’adin ya cika.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!