Labarai
Rundunar Sojin Najeriya ta karbi ’yan ta’adda 11 da suka miƙa wuya

Rundunar Sojin Najeriya ta karbar ’yan ta’adda 11 da suka miƙa wuya.
Bayanin hakan na kunshe a cikin sanarwar da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labaran Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta ce ’yan ta’addan sun miƙa wuya ne a tsakanin ranakun 15 zuwa 22 ga Satumbar da muke ciki.
Haka zalika ta ce a cikin wannan lokaci rundunar ta ƙwato mota, harsasai da wasu kayayyakin aiyyukan ta’addanci.
Rundunar ta kuma sha alwashin ci gaba da fatattakar ƴan taʼadda.
You must be logged in to post a comment Login